A cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu bayan dawowarta daga Najeriya inda taje domin ganin 'yammatan Chibok da kungiyar Boko Haram ta saki, 'yar majalisa Frederica Wilson tace zai yi wuya 'yan majalisar su mance dabanbancin siyasa kan batun DACA. Grace ta tambayeta:
Kina Gani Jam'iyun siyasar nan biyu zasu iya hada kai su samar da tsari da zai zama da taimako ga wadannan mutanen da ake kira DreaMers?
Zai zama da wuya saboda irin akidar wassu ‘yan majalisunmu wadanda ke tunanin zaman kaka gida na maida Amurka launin kasa-kasa kuma basa son haka, suna son in sun ce a sake maida Amurka babba, suna nufin a sake maida Amurka fara.
Saboda haka yana da matukar wahala a shawo kan mutane wadanda ked a irin wannan rashin fahinta a cikin zukatansu saboda da haka suka tashi kuma abinda suka yi imani dashi kenan, kuma suna wakiltar wadanda suka yi imani da shi.
Don haka in ka wakilci mutanen da suka yi imani da hakan, zaka yi zabe ne ba kadai saboda lamirin ka ba, har ma da lamirin wadanda kake wakilta.
Saboda haka sai mun sami tattaunawa da basira kan su wanene masu hangen nesa, sai mun sami kowane mutum da mai yiwuwa zai iya jefa kuri’ar A’A, kan a kalla rabin tattaunawa da masu hangen nesa na zahiri, ya sadu dad a mai hangen nesa fuska da fuska, ya suarari labarin, ya suarari inda aka kai, ya saurari fatarsu, burinsu, kila zaka taba zuciyar yan majalisun da aka aika majalisar, su yi wani abu daban, kila zaka chanza tunaninsu, saboda al’amarine dake kwan gaba kwan baya a matakin jihohi, shiyya da gwamnatin tarayya, tsararraki da dama, kuma ban taba ganinshi da muni kamar yanzu ba.
To menene zaki gayawa wadannan dake cin moriyar shirin da suke daukarki uwa abin koyi?
Ina gaya musu kamar yadda na fada musu a majalisar jaha cewa suna da rayuwa a gaba, kuma suna da mutane dake kaunarsu kuma suna da mutane dake goyon bayansu, don haka dole ne mu hadu mu yaki, mu kuma chanza tunanin mutanen da basu fahinta ba.
Basu kada kuri’ar haka saboda basu fahinta ba, ba abinda suka saba dashi bane, kuma basu da sha’awar kada kuri’a da zai sabawa wadanda suka zabasu saboda suna bukatar cin zabe kowace shekara.
Don haka sai ka shiga zuciyarsu da tunaninsu, su jajirce, su ci gaba da rubuta wasiku, su yi amfani sa shafukan sada zumunta, su ci gaba da kasancewa manyan misalai wa tsararrakinsu saboda mu sami manyan abin kwatanci da zamu basu goyon baya wadanda zamu rike hannunsu muce Malam dan majalisa? Ka sadu da mai hangen nesa. Wannan shine mai hangen nesa. Baka taba saduwa da mai hangen nesa ba. Ka dai ji Kalmar hangen nesa ne, amma ga mai hangen nesa na zahiri.
Idan har dukkanmu zamuyi haka? Mu ci gaba da yi musu yaki? Kamar yadda mukasan abinda ya faru da ‘yan’matan nan dari uku a daji har shekaru uku amma suna da rai? In harm un iya fitar dasu daga daji a Najeriya daga Boko Haram? Lallai zamu iya dokar da zai taimakawa masu hangen nesa.
Wakiliyarmu Zainab Babaji ta fasara ta kuma karanta bayanin 'yar majalisa Frederica Wilson
Your browser doesn’t support HTML5