Zafafan Kalamai Kan Iya Tayar Da Hankalin Al’umma - Masana

'Yan sandan Najeriya yayin kaddamar da rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Enugu (Twitter/@PoliceNG)

Kwanaki kalilan kafin zaben gwamnoni da ‘yan Majalisun Dokoki a wasu jihohin Najeriya, an fara samun zafafan kalamai wadanda masan ke ganin idan ba’a dakile su ba, za su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.

Daya daga cikin abubuwan da ke saurin harzuka jama’a, musamman mabiya addinai shine yin kalamai da suka shafi addini, wanda wasu ‘yan siyasa kan yi amfani da su don rarraba kawunan al’umma da zummar cimma burinsu, kamar yadda masu fashin baki suka sha fada.

Jahar Nasarawa da ke da tarihin zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, a wannan kakar zaben, an fara samun cece-kuce da ke rura wutar rikicin da wasu ke ganin na iya rikidewa zuwa tashin hankali ko wata matsala.

Shugaban kungiyar hadin kan kirista a jihar Nasarawa, Veri Rabaran Fada Sunday Emma, ya ce ba su bukatar wani yanayi da zai lalata zamantakewar su.

Shi ma sakataren kungiyar JNI a jihar, Imam Muhammad Ali ya ce suna fadakarwa sosai kan zaman lafiya.

Gwamnan Jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a jihar, ya ce al’ummar Nasarawa na zaune lafiya da junansu da ke da bambancin addinai.

A Jihar Filato kuwa, an sami irin wadannan cece-kucen, wanda dan takarar gwamna a jami’iyyar PDP, Barista Caleb Mutfwang, ya roki jama’a su kwantar da hankalinsu.

A shekarun baya irin wadannan kalamai marasa dadi sun haddasa mummunan rikicin bayan zabe, da ya kai ga rasa rayukan jama’a da salwantar dukiyoyi masu tarin yawa.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Zafafan Kalamai Kan Iya Tayar Da Hankalin Al’umma - Masana - 3'13"