Zaben Raba Gardama A Mali Ya Bar Baya Da Kura

Zabe a yankin Kidal

A jamhuriyar Nijar masu bin diddigin al’amuran yau da kullum na bayyana mabambantan ra’ayoyi game da zaben raba gardamar da aka gudanar a jiya Lahidi 18 ga watan Yuni a Mali.

A yayinda wasu ke ganin abin a matsayin matakin share fagen zabubbukan da za su bada damar mayar da mulki a hannun farar hula, wasu na cewa rashin gudanar da zaben a yankin Kidal sanadiyyar matsalolin tsaro babbar matsala ce da ka iya shafar halaccin sakamakon da za a bayar.

Karon farko kenan da ‘yan Mali ke halartar runhunan zabe tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Ogustan 2020.

Zaben, wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana kwam gaba kom baya kafin a fitar da ranar gudanar da shi, ya wakana cikin kwanciyar hankali a cewar rahotanni abinda matemakin shugaban gamayyar kungiyoyi ta FCN, Abdou Elhadji Idi, ke kallonsa tamkar wani cigaba a yunkurin mayar da kasar ta Mali kan tafarkin dimokradiya.

Wasu masu zabe

Kungiyoyin sa ido sun ayyana cewa kasa da kashi 30 cikin 100 na al’ummar Mali million 8.4 da suka yi rajista ne suka fito don kada kuri’a a wannan zabe a yayin da a yankin Kidal dake karkashin ikon ‘yan ta’adda ba a yi zaben ba haka kuma wasu kungiyoyin fafutika mambobin hadakar M5 RFP, a karkashin jagorancin malamin addinin islama Mahmoud Dicko, su ka yi tur da kundin tsarin mulkin da gwmamantin rikon kwaryar Malin ke fatan kaddamarwa ta hanyar wannan referendum abinda ka iya shafar halaccin kundin a idon duniya. Editan jaridar la Roue de l’Histoire, Ibrahim Moussa, shi ne magatakardan kungiyar ‘yan jarida masu kula da sha’anin tsaro RJPS.

Ana sa ran fitar da sakamakon wucin gadi a tsakanin Talata 20 zuwa Laraba 21 ga watan yuni kafin a gabatar da shi wa kotun tsarin mulki wace ke da hurumin bayar da sakamakon dindindin.

Wannan Sabon babin siyasar da aka bude a Mali na zuwa ne a wani lokacin da gwamnatin mulkin soja a karkashin Colonel Assimi Goita ta bukaci rundunar tsaro ta MDD wato MINUSMA ta fice daga kasar saboda zarginta da gaza magance matsalolin ta’addancin da aka shafe shekaru 10 ana fuskanta a kasar wadanda kuma su ka bazu zuwa kasashe makwabta.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Raba Gardamar Mali Ya Bar Baya Da Kura