Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka nemi kujerar shugaban jam’iyar PDP mai adawa a Najeriya sun ce ba su amince da sakamakon zaben da ya bai wa Prince Uche Secondus nasara ba.
Secondus daga yankin kudu maso kudancin Najeriya, ya samu kuri’u 2,000 cikin kuri’au 2,296 da aka kada.
Hakan ya ba shi nasara akan abokan takararsa biyu Farfesa Tunde Adeniran da Chief Raymond Dokpesi.
Adeniran ya samu kuri’u 230 yayin da Dokpesi wanda ya yi fice wajen sana’ar kafafen yada labarai ya samu 66.
Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadannan ‘yan takarar biyu, sun bayyana wa manema labarai a hira daban-daban da suka yi cewa ba su amince da sakamakon ba.
A cewarsu wani jerin sunaye da aka fito da su aka bai wa wakilan da za su yi zabe mai taken “unity list” shi suka ce ya birkita al’amura.
To amma ga wasu ‘yan jam’iyar ta PDP zaben sahihi ne.
“Tun da aka samar da PDP, ba a yi zabe daidai kamar irin wannan ba wanda aka yi shi akan Gaskiya akan turbar dimukradiyya.” Inji Ibrahim Kazaure, shugaban jam’iyar PDP a arewa maso yamma.
“Ni ina ganin ba wai taron ya bar baya da kura ba ne, dukkan wanda bai ji dadin wannan abun ba, zai kasance mutum ne da zai hakikance akan sai ya samu abinda yake so.” Inji Hassan Muhammad Baba.
Tun gabanin taron, wasu daga cikin wadanda su ka ayyana tsayawa takarar da suka hada da Bode George da Gbenga Daniel suka janye.
Shi dai George ya yi zargin cewa gwamnan Rivers Nyesom Wike ya nunawa Yarbawa wariya musamman don mara baya ga Secondus.
Babban taron na PDP shi ne na farko, tun bayan da ta shiga rudanin shugabancin bayan da ta sha kaye a hanun jam'iyar APC mai mulki.
Wannan zabe na nufin aikin kwamitin rikon da Sanata Ahmed Makarfi ke jagoranta ya kawo karshe.