Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da ya canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa ta PDP, babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida a Minna.
Baicin cewa Janar Babangida tsohon shugaban mulkin soja ne da ya dade yana mulkin kasar, jigo ne a jam'iyyar ta PDP kuma ana harsashen duk wanda ya goyi bayansa zai kai labari gida.
Shugabannin biyu sun kwashe kimanin sa'o'i hudu suna ganawa. Amma da suka gama babu wanda ya cewa manema labarai uffan.
Amma masu nazarin siyasar kasa suna ganin Alhaji Atiku Abubakar ya je Minna ne ya kama kafar Janar Babangida domin ya cimma burinsa, wato jam'iyyar PDP ta bashi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.
A daya gefen kuma shugabannin jam'iyyar PDP reshen jihar Niger na harsashen ganawarsu na da alaka da babban taron jam'iyyar da za'a yi gobe Asabar a Abuja, tara ga watan Disamban nan, kamar yadda daya daga cikin jigon jam'iyyar a jihar, Yahaya Ability ya bayyana.
A cewarsa abun dake gabansu shi ne yadda za'a yi zaben ranar Asabar ba tare da samun yamutsi ba. Ya ce abun da ya kawo Atiku Abubakar ke nan zuwa ganin Janar Babangida domin a samu masalaha.
Tsohon gwamnan jihar Niger Dr. Muazu Babangida Aliyu shi ne shugaban kwamitin dake shirya taron Abujan, ya ce sun kammala shiri tsaf.Ya kuma musanta labarin da ake yayatawa na cewa Atiku Abubakar ba zai kada kuri'ar zaben shugabannin jam'iyyar ba wanda za'a yi gobe. Ya ce karya ne. Duk wanda ya zo kafin wata daya da zaben yana da hurumin jefa kuri'a amma ba za'a ba kowa fifiko ba ko a dakatar da wani sabili da wani mutum ba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum