Arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga da kuma rashin bude runfunan zabe a wuraren da ‘yan hamayya suka fi karfi, sun kawo cikas a zaben shugaban kasar da ake sake gudanarwa a kasar Kenya.
‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa kan masu zanga zanga a Kibera, wata unguwa dake Nairobi babban birnin kasar, lokacin da suke kokarin kafa shingaye a kofar runfunan zabe.
‘Yan sanda sun harbe suka kashe wani mutum a Kisumu yayin wata arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga, bisa ga wata majiyar ‘yan sanda a yankin.
Duk da zanga zangar da yunkurin gurguntar da zaben, wadansu masu kada kuri’a suna begen ganin an sami hadin kan kasa.
"Fatar da muke yiwa kasar ita ce, ko da wanene ya lashe zabe, zai iya hada kan kasar da ‘yan siyasa da siyasa suka rarraba".
Makonni biyu da suka shige shugaban adawa Raila Odinga ya janye takararsa bisa hujjar cewa, babu abinda ya sauya a hukumar zaben kasar da ake kira IEBC. Ya kuma fitar da sanarwa a jajibirin zaben yana kira da a hada kai wajen kin amincewa da zaben.