A Najeriya hukumar zabe ta kasa ko INEC a takaice ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Osun da za'a yi ranar tara ga wata mai zuwa.
Hukumar tace zata yi shirye-shirye domin tayi nasara irin wadda aka yi a jihar Ekiti da hukumar tace gagarumar nasara ta samu. Tace har yanzu babu wanda ya kai hukumar kara akan ko an yi rashin gaskiya ko kuma an tafka magudi.
Bayanin ya fito ne daga shugaban hukumar mai zaman kanta Farfasa Attahiru Jega wanda yace duk shirye-shiryen da yakamata a yi zasu tabbatar an yi shi domin abun da ya faru a jihar Ekiti ya kasance zakaran gwajin dafi ga hukumar. Yace za'a samu nasaar zabe ba tare da an yi rigimar zuwa kotu ko koke-koke na cewa an yi rashin gaskiya ko magudi ba.
Farfasa Jega yace zaben da suka yi a jihar Ekiti ya samu inganci fiye da zabubukan da suka yi can baya. Sabili da ingancin zaben kawo yanzu babu wanda ya zargi hukumar da aikata rashin gaskiya. Duk wasu koke-koken da suke ji ya shafi abun da aka ce jami'an tsaro sun yi ne amma ba hukumarsu ba. Shi kansa dan takarar da aka kayar yace ya yadda da sakamakon zaben. Ita ma jam'iyyar gwamnan da ya fadi tana kokarin zuwa kotu amma ba akan sakamakon zaben ba.
Akan sanadiyar nasarar da suka samu shugaban hukumar zaben yace gaskiya ingancin tsarin da suka yi ne ba lallai sabili da jami'an tsaro ba. Yace abubuwa ne da suka dade suna shiryawa da yin nazari a kai. Abu dake tafe dashi shi ne fara shirye-ahirye da wuri shi ma ya kawo ingancin zaben. Akwai kuma lokacin da suka dauka suka bayar da cikakkiyar horaswa ga ma'aikatansu. Su kansu jami'an tsaro sun taka rawa gani duk da korafin da wasu suka yi a kansu. Kasancewar jami'an tsaro ya sa ba'a samu hargitsi ko yamutsi ko fadace-fadace ba ko kuma wani magudin zabe ba.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5