Wasu masu fashin baki dai na ganin Zaben shugaban kasar Amurka na wannan mako ya jawo hankali 'yan Afirika da dama saboda wasu manyan dalilai. Lawya mai zaman kanshi a Kaduna, Barr. El-zubair Abubakar na cikin masu nazari gameda Zaben na Amurka.
Ya ce zaben Amurka yafi maida hankali a kan batun yaki da murkushe ayyuakn ‘yan ta’adda musamman tun lokacin da shugaba Bush ya karbin mulkin kasar daga hannun Ragan. Amma a yanzu zaben ya karkata ne a kan abubuwa dake faruwa a gida.
Yanayin gudanar da zaben America da kuma lamurran da kan biyo bayan Zaben na cikin abubuwan da ke jawo hankali wasu 'yan-Najeriya.
Galibin ‘yan Najeriya sun sha’awarsu a kan yanda ake gudanar da zaben Amurka har a bayyana wanda ya yi nasara ba tare da samun tashin hankali ba. Sun kuma yabawa kyakkyawar mu’amala tsakanin ‘yan takara ba kamar Najeriya ynda ake daukar abokin takara a matsayin abokin gaba.
Wasu 'yan-Najeriya dai na ganin Najeriya na da darasin da za ta dauka gameda Zaben na Amurka.
Gobe Talata 3 ga watan Nuwamban nan ne dai za a kada kuri'ar Zaben shugaban kasar Amurka tsakanin Donald Trump na jamiyyar Republican mai Mulki da kuma Joe Biden na Democrat.
Ga dai rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Nageriya:
Your browser doesn’t support HTML5