ZABEN AFIRKA TA KUDU: Jam'iyyar ANC Ta Samu Kasa Da Kashi 50% Na Kuri'un Da Aka Kirga

SAFRICA-ELECTION/

Ana sa ran fitar da cikakken sakamakon zaben a karshen makon nan da mu ke bankwana da shi.

Bayan da aka kirga sama da kashi 65% na kuri'un da aka kada a larduna tara na kasar, jam'iyyar ANC wacce ke da rinjaye tsawon shekaru 30 tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata ta samu kasa da kashi 42% na kuri'un da aka kada a zaben, bisa ga wani bangare na sakamakon zaben yayin da aka ci gaba da kirgawa.

Sakamakon kuri'ar ya nuna cewa ANC za ta iya yiwuwar gaza samun rinjaye a majalisa, a karon farko cikin shekara 30 da suka gabata, lamarin da zai tilasta mata kulla hadaka.

Jam'iyyar ANC ta rasa goyon bayan jama'a ne saboda karuwar rashawa da laifuka da kuma rashin aikin yi.

Ana sa ran fitar da cikakken sakamakon zaben a karshen makon nan da mu ke bankwana da shi.