Zaben 2023: Tarihin Siyasar Jihar Benue

Kayan Marmari

A yayin da ake daf da gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, akwai muhimman bayanai dabam-daban a kan jihohin Najeriya da irin abubuwan da suka bambanta su da juna.

Benue, jiha ce da aka kirkira a shekarar 1976 wacce ke daya daga cikin jihohin Arewa ta tsakiya a Najeriya, jihar na da yawan jama'a kusan miliyan 4 da 253,641 bisa ga alkaluman kidayar jama'a da aka yi a shekarar 2006.

Jihar ta samo sunanta ne daga kogin Benue, wanda shi ne kogi na biyu mafi girma a Najeriya. Kuma ta yi iyaka da jihohi shida wadanda suka hada da Nasarawa daga bangaren Arewa, Taraba daga Gabas, Kogi daga Yamma, Inugu daga Kudu-maso-Yamma, Ebonyi da Cross Rivers daga Kudu. Kuma ta hada iyaka da kasar Kamaru.

Gabar kogin Benue

Kabilun Tiv, Idoma da Igede ne kabilu mafi girma a jihar. A cikin kananan kabilun Benue akwai Etulo, Igbo, Jukun da dai sauransu. Babban birnin jihar shi ne Makurdi.

Benue jiha ce da ake mata taken matattarar abincin Najeriya Saboda arzikin noma. Amfanin gona da aka fi nomawa a cikinta sun hada da lemun zaki, mangwaro, dankalin hausa, rogo, waken suya, dawa, ridi, shinkafa, gyada da kwakwa.

Mangwaro

Abdullahi Shelleng, shi ne gwamnan soja na farko a jihar ta Benue wanda ya fara aiki daga ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar 1976 zuwa Yuli na shekarar 1978 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo, bayan da aka cire jihar Benue daga tsohuwar jihar Benue-Filato.

Bayan Shelleng gwamnoni 12 ne suka mulki jihar zuwa shekarar 1999. Goma daga cikinsu sojoji ne sannan biyu kuma farar hula.

Bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, George Akume ya dare kan karagar mulkin jihar a matsayin gwamna a karkashin jam’iyyar PDP daga watan Mayun 1999 zuwa Mayu na shekarar 2007, daga nan sai Gabriel Torwua Suswam shi ma daga jam’iyyar PDP daga shekarar 2007 zuwa Mayun 2015, sai kuma gwamna da ke daf da kamalla wa’adin mulkinsa karo na 2 wato Samuel Ioraer Ortom wanda daga APC ya koma PDP, ya karbi mulki daga watan Mayun shekarar 2015 zuwa yau.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

A zaben gwamnan jihar Benue mai zuwa na watan Maris din shekarar 2023, ’yan takara da ke kan gaba sune; Hyacinth Alia da mataimakinsa Sam na APC wanda kotu ta soke zaben fidda gwanin da ya samar da su a matsayin ‘yan takara sakamakon rashin bin ka’ida a wajen gudanar da sahihin zaben fidda gwani kamar yadda dokar zabe ta shekarar 2022 da aka yi wa kwaskwarima ta tanadar, sai dan takarar jam’iyyar PDP Titus Uba wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar da mataimakinsa Sir John Ngbede, sai Herman Hembe da Christopher Onyiloyi Idu na jam’iyyar Labour, daga nan kuma sai Bem Reuben Angwe da Comfort Ogbaji na jam’iyyar NNPP da dai sauransu.

katukan zabe

Ya zuwa yanzu dai, ‘yan asalin jihar da ma mazauna na ci gaba da bayyana cewa abubuwan da suka fi ci musu tuwo a kwarya su ne rashin tsaro, matsin tattalin arziki, koma baya a aikin noma, rashin aikin yi ga matasa da dai sauransu.

Mazauna jihar sun tofa albarkacin bakinsu game da tsare-tsaren da hukumar INEC ke yi don gudanar da zabe da kuma shirin da masu kada kuri’a suke yi don tunkarar zaben.

Ahmed Mohammed, da ke aikin kanikanci a birnin Makurdi ya ce bashi da kwarin gwiwa a kan zaben, saboda har yanzu galibin mutane basu karbi katin zabensu ba, abin da ya kamata su samu watanni uku kafin zaben.

Saurari rahoton Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben 2023: Tarihin Siyasar Jihar Benue