Zaben 2023: Siyasar Jihar Kaduna

Mando Nigeria

Tsohuwar jihar Arewa a karkashin Lord Frederick Lugard, ita ce ta koma jihar Arewa ta tsakiya a alif 1967 kafin daga bisani ta zama jihar Kaduna a 1975. A alif 1987 ne kuma aka cire jihar Katsina daga tsohuwar jihar ta Kaduna, wadda a yanzu ke da kananan hukumomi 23.

Kafin zuwan wannan jamhuriya a alif 1999, dimokaradiyya ta yi ta yin tuntube da fuskantar juyin mulki daga sojoji, sai dai tun shigowar wannan jamhuriya zababbun gwamnoni ne ke mulkin jihar kuma zabubbuka biyar aka gudanar sannan a wannan shekara ta 2023 ne za a yi zabe na shida ba tare da wani katsalandan ba.

Sabanin wasu jihohin Najeriya da gwamnoni uku ne suka yi mulki cikin wadannan shekaru saboda kowanne wa'adin shekaru 8 yayi, a jihar Kaduna gwamnoni biyar aka yi cikin wannan jamhuriya sakamakon baiwa gwamnan da aka zaba a shekarar 2007 mukamin mataimakin shugaban kasa bayan shafe shekaru biyu a matsayin gwamna, da kuma mutuwar tsahon gwamna Patrick Ibrahim Yakowa da ta sa aka rantsar da mataimakin shi Mukhtar Yero a matsayin gwamna.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Patrick Ibrahim Yakowa

Zaben shekarar 2023 a jihar Kaduna dai ya zo da sabon salo musamman ganin yadda manyan jam'iyyun siyasa suka zabo 'yan takararsu a jihar, inji mai fashin baki kan siyasar Najeriya, Barr. El-Zubair Abubakar.

El-Zubair ya ce a wannan karon an sami ‘yan takarar gwamna biyu daga karamar hukuma daya kuma dan takarar da jam'iyya mai mulki ta tsayar karamar hukumar daya ya fito da gwamna mai ci, wanda zai cika shekaru 8 zuwa watan Mayun bana.

Dagewa kan amfani da na'ura wajen tattara sakamakon zaben bana na daga cikin batutuwan da ke daukar hankali a jihar Kaduna kamar yadda Barr. Mohammed Ibrahim Zariya ya bayyana.

Na'urar tantance katin zabe

Barista Ibrahim Zariya ya ce satar akwatunan zabe da amfani da kudi ba za su yi tasiri ba a zaben wannan shekarar saboda amfani da na'urar BVAS.

Duk da matsalolin tsaro da kuma zuwan sabon salon saka na'ura wajen zaben bana, al'umar jihar Kaduna sun ce suna sa ran zaben ba zai zo da wata tangarda ba.

A zabubbukan baya dai mafi akasari jam'iyyu biyu ne masu karfi kan fafata, sai dai kuma a wannan karon zancen ya sha bamban, saboda jam'iyyu biyar masu karfi da zasu fatata a jihar Kaduna.

Da yawan al'umar jihar Kaduna dai sun bayyana bukatar ganin duk wanda ya zama gwamnan jihar, ya maida hankali akan tsaro, ilimi da tattalin arziki.

Wannan ne karon farko da za a yi amfani da na'ura wajen tattara sakamakon zabe kuma jihar Kaduna na cikin jihohin da gwamna mai ci ke karkare wa'adinsa na shekaru 8, a saboda haka kowacce jam'iyya ce ma ta ci zabe sabon gwamna za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara ta 2023.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben 2023: Siyasar Jihar Kaduna