ZABEN 2023: Hukumomin Saudiya Sun Kama A Kalla Mutane 30 Da Laifin Daga Hoton 'Yan Siyasa A Ka'aba

Hukumomin Saudiyansun cafke wadansu 'yan Najeriya da laifin daga hutunan 'yan siyasa a dakin Ka'aba.

Yan Najeriya wadanda suka samu damar kai ziyarar aikin Umrah na bana a kasar saudiyya sun yi tsokaci game da zargin cafke wasu yan’Ƙasar da hukumomin Saudiyar suka yi bisa laifin daga hotunan yan siyasa dake neman takarar shugabanci a Najeriya a Harami yayin gudanar da dawafi a gaban dakin ka’abah

Rahotonin dake fitowa daga kasar Saudiyya dai ya yi nuni da cewa hukumomi a ƙasar sun cafke wasu 'yan Najeriya da ake zarginsu da wuce gona da iri wajen shiga tare da daga hotunan wasu 'yan siyasa dake neman tsayawa takarar shugabanci a gaban dakin Ka'aba.

Murtala Adamu jega Murson Dan siyasa ne a Najeriya wanda yace shi ganau ne na lamarin. Yace lamarin na iya bata sunan kasar. Bisa ga cewarsa, kamata ya yi a ce masu aikin hajin sun dauki lokaci su yi addu'a a sami zaman lafiya da tsaro a kasar ba yi wa masu neman tsayawa takara addu'a ba.

Wasu na ganin 'yan siyasar ne suka biyawa magoya bayansu kudin zuwa aikin Umrah da nufin rokon Allah don samun nasara a babban zaben kasar da ke tafe.

Hukumomin Saudiyansun cafke wadansu 'yan Najeriya da laifin daga hutunan 'yan siyasa a dakin Ka'aba

A halin da ake ciki dai majiyar daga Saudiya ta bayyana cewa wadanda aka kama suna hannun mahukunta kasar, karkashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata.

Tun dai a cikin watan Ramadana aka yi ta hango yadda wasu 'yan Najeriya da suka dinga tallar 'yan siyasar kasarsu a garin makkah, lamarin da hukumomi a kasar suka ce baza su lamunta ba.

Saurari cikakken rahoton Shamsiya Hamza Ibrahim cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Saudiyansun cafke wadansu 'yan Najeriya da laifin daga hutunan 'yan siyasa a dakin Ka'aba

Ku Duba Wannan Ma Zaben 2023: Ya Cancanta Goodluck Jonathan Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa?