Shugaba Jonathan yace tun zaben 2011 yayi alkawarin gudanar da zabe mai inganci kuma yace idan ya fadi zai mika ragamar mulki ga duk wanda ya samu nasara.
A cikin zantawarsa da manema labarai shugaba Jonathan ya mayarda hankalinsa ne akan harkokin tsaro fiye da batun zaben Najeriya. Amma ya bada tabbacin za'a gudanar da zaben kamar yadda aka shirya kuma za'a rantsar da duk wanda yayi nasara ranar 29 ga watan Mayu nan wannan shekarar.
Aliyu Sarkin Fada ya kalli kuma ya saurari jawabin shugaban kasar. Yace cikin maganganunsa akwai wadanda ya kama kamar inda yace idan ma bai ci zaben ba zai sauka ya bada mulki.Sabili da kalamun Aliyu na ganin lamarin ya soma tsorata Jonathan shi yasa yayi kalamun. Da alama yana shakkun zaben.
Shi kuma wani Tela Kabiru Mai Yadi yana fatan alwashin na shugaba Jonathan zai zama gaskiya. Yana fatan Allah yasa a yi zaben lafiya. To saidai yace a hakikanin gaskiya zuciyarsa bata yadda da mutanen Jonathan ba cewa zasu gudanar da zaben domin karya a wurinsu abu karama ce.
To amma mataimakin daraktan kemfen din Jonathan Isa Tafida Yariman Muri yace jawabin na Jonathan zai kawar da rade-radin da ake yi cewa gwamnati ba ma zata bari a yi zaben ba. Yace mutane suna ta fadan abu da babu shi a tsarin mulkin kasar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5