A jihar Neja da misalin karfe sha biyun daren jiya aka kammala tara sakamakon zaben daga duk kananan hukumomin jihar.
Jinkirin da aka samu daga wasu kananan hukumomi ya sa ba'a samu sakamakon ba akan lokaci. Baturen zaben Farfasa Abdulganiyu Hambali yace sun gama tattara sakamakon daga kananan hukumomi 25 dake jihar.
Farfasa Hambali ya bayyana sakamakon inda yace APC ta samu kuri'u dubu dari shida da saba'in da bakwai da dari shida da saba'in da takwas yayinda PDP ta samu dubu dari daya da arba'in da tara da dari biyu da ashirin da biyu.
Jami'in hukumar zaben a jihar Neja Madaki Muhammad Wase ya bayyana dalilan da suka sa aka samu jinkirin tattara sakamakon a jihar Neja. Yace a shekarun da yayi yana aiki a INEC bai taba ganin inda jama'a suka fito yin zabe ba irin wannan. Yace mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu. Yace har ya kai ana ta jefa kuri'a har shabiyun dare zuwa karfe daya. Yace an wayi gari a wasu wuraren ana jefa kuri'a. Yace a cikin irin wannan yanayin ba za'a rasa wasu matsaloli ba kodayake ba zasu yi tasiri ba akan sakamakon zaben.
Muhammad Wase yace a wasu wurare wasu mutane da basu kayauatatawa karsar da kuma kansu sai sun sace akwatunan zabe.
Kujerun 'yan majalisar dattawa da majalisar wakilai duk APC ce ta lashesu a jihar Neja.
A jihar Kogi ma APC ce ta lashe kujeru uku na majalisar dattawa kana ta samu kujeru shida na majalisar wakilai. An bar PDP da kujeru uku kawai.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5