Masana sun gano kwararan dalilan da suka kaiga sakamakon da aka samu a zaben baya kuma suna iya su yi tasiri a zaben 2015.
WASHINGTON, DC —
Majiya: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta.
Ta ko ina, ranar 28 ga watan Maris ne ranar da Najeriya zata fuskanci lokaci mafi dar-dar na babban zaben Kasar tun bayan da aka dawo kan turbar mulkin dimukuradiyya a a kasar, wanda a yanzu ya shafi dukkan kasashen nahiyar Afrika ta yamma da sauran nahiyoyin da kowa ke tofa albarkacin bakinsa. Wannan ,shine karo na biyu da za’a kara neman takarar tsakanin Shugaban Kasa mai ci yanzu Jonathan Goodluck na jam’iyyar PDP mai mulkin kasar da kuma abokin karawarsa daga Jam’iyya APC wato Muhammadu Buhari. A shekarar 2011 ne dai suka kara tsakanin Jonathan, Kiristan Kudancin Najeriya daga yankin Neja Dalta mai arzikin man fetur da kuma shi Buhari Musulmin Arewacin Najeriya dan asalin Jihar Katsina kuma tsohon shugaban kasa a karkashin mulkin soja na gajeren lokaci a farkon karni na 80. Goodluck ya yi gagarumar nasara da Kason kuri’u 58.9 shi kuma Muhammadu da kaso 31.9.
Salon zaben na 2011 a dukkannin Jihohin Kasar 36 yana cike ne da matsalolin bangaranci, kabilanci da kuma bambancin addini daga dukkan bangarorin adawa da juna. Sannan wasu da dama daga cikin ‘yan jam’iyyar CPC a lokacin sun kewaye ta hanyar goyon bayan kai tsaye ko a kaikaice ga jam’iyyar PDP mai mulkin kasar. Bayan hukumar zaben kasar ta bayyana Jonathan a matsayin wanda ya yi nasara, magoya bayan Buhari sun zargi cewa an yi magudi wanda hakan ya haifar da rikicin da aka rasa rayukan daruruwan jama’a. A wannan shekarar kuma sai ‘yan adawar Goodluk suka hade kai wajen marawa Buhari da kuma Jam’iyyar PDP baya. Hakan yay a kawo gagarumin canjin alkibla a ci gaban siyasar Najeriya inji shugaban cibiyar Afrika Peter Pham dake da mazauni a Washington dake Amurka. Farkon abinda ake sa ran zai iya haifar da zahirin tsarin jam’iyyu biyu. Wannan na nufin zama zaben da yafi ko wane zama cike da gasa mai zafi tun bayan zaben shekarar 1999.
Shekaru da dama siyasar Najeriya na fuskantar barazanar amfani da kabilanci da addini wajen tarwatsa hadin kan mutane kamar yadda wani mai fashin bakin al’amuran siyasa Dakta Kabir Mato ya bada misalin cewa, a shekarar 2011 jam’iyyar adawa ta CPC ta she wuya a hannun ta PDP mai mulki bayan watsa jita jitar cewa jam’iyyar adawar ta ‘yan arewa ne kuma musulmai. A inda CPC din ta kai da lashe Jihohi 10 zuwa 12 ita kuma PDP ta ci Jihoihi 6 zuwa bakwai amma kuma ita ta kai ga nasara. Pham yace duk da yake ba wa za a iya cewa baya zata haifi gab aba, to amma Buharin na kewaye da kalubalen harzukawar ‘yan PDP, adawa, rashin cancantar Jonathan, to amma ba zamu iya kirga mutane da ke fargabar tunawa da yadda Buharin ya taba mulkar kasar ba a mulkin Soja. BA kididdiga bace amma ta faru akan mutane da yawa sun fada wannan tunani na salon mulkin Buhari.