Farfasa Attahiru Jega shugaban hukumar zaben Najeriya ya ja kunnuwan 'yan kasar da su yi watsi da duk wani sakamakon zabe da ake yadawa a kafofin internet na sada zumunta ko Facebook.
Baya ga haka matasan sun yi anfani da damar da wasu gidajen radiyo masu zaman kansu irin su Radio Freedom da Radio Rahama duk a Kano suka baiwa masu saurarensu inda suka hada tashoshinsu na yada shirye-shirye kai tsayeda zauren INEC da ake sanarda sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.
Wani matashi yana talla kuma yana sauraren sakamakon zaben daga gidan radiyo da wayar hannunsa. Yace kamar yadda INEC tace su gujewa jita-jita ya kamata ya ji abun da hukumar ke sanarwa jama'a game da zaben. Shi ma wani mai sayar da katin wayar tafin hannu ya makala wayar sauraren radiyo a kunnensa yana sauraren sakamakon zabe.
Matasan sun ce suna jin sakamako kai tsaye ba tare da wata buya-buya ba.. Wannan ya nuna wayewar da matasan yanzu suke dashi gameda kafofin yada labari na zamani da kuma yadda ake tafiyar da harkokin da suka shafi kasarsu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5