To saidai shugaban jam'iyyar MNRD Hakuri, Muhammad Usman ya koka da cewar a wasu wurare an samu matsaloli har ma ana sayen kuri'u.
Muhammad Usman yace yana fadan abun da ya samu hakikanci akansa ne. Kuri'un wasu 'yan takara basu isa wani wuri ba. Wasu kuma sun isa amma ba isassu ba.Akwai kuma sayen kuri'u.
Inji Muhammad Usman yace kuri'un jam'iyyarsa an sasu kasuwa. Ana tare masu zuwa rumfunan zabe ana sayen kuri'un.
A wani halin kuma Bukari Sani Zilli na jam'iyyar PNDS Tarayya ya mayar da martani inda yace mutane yakamata su yi aiki da dimokradiya da doka. Bayan an rufe kemfen har ranar zabe 'yan adawa suna tsaye suna kemfen. Wai suna tare mata da matasa suna gaya masu jam'iyyar da zasu jefawa. Yace sun kuma san sanu daba daladala daridari domin a jefa masu kuri'u.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5