Zabe da 'Yan Gudun Hijira

Wasu 'yan gudun hijira

Wata mai zuwa za'a gudanar da zabe a Najeriya lamarin da ya sa wasu suna tababar cancanta ko rashin cancanatar yin zabe a sansanonin 'yan gudun hijira

Ra'ayin 'yan siyasa da dama ya banbanta akan cancanta ko rashin cancantar gudanar da zabukan a sansanonin 'yan gudun hijira musamman na jihar Borno.

Wasu 'yan jihar Borno suna ganin bai kamata a yi ma batun gudanar da zabe ba a sansanonin 'yan gudun hijira a jihar Borno. Amma kuma wasu na ganin yin zabukan ne kadai zai kawo saukin lamarin da aka shiga.

Malam Adamu Dan Borno yana cikin masu ra'ayin kada a gudanar da zabe a sansanonin 'yan gudun hijira. A ganishi ma gudanar da zabe a jihar bashi ya kamata a yi ba domin wai 'yan siyasa sun maida hankali ne akan zabukan dake gabansu sun tura matsalar da jama'a ke ciki bayansu. Maimakon zabe a nemi zaman lafiya tukunna. Abun takaici shi ne gwamnati bata mayarda hankal akan yadda za'a mayarda mutane gidajensu ba.

Sanata Ali Ndume yace shi zabe bai dameshi ba saidai akwai wasu 'yan siyasa da suke son su leko jihar lokacin zabukan su wawure akwatunan zabe su yi tafiyarsdu. Irinsu suna barazana zasu karbe mulkin jihar.

Barrister Ibrahim Birma mataimakin dan takarar gwamnan jihar Borno na jam'iyyar PDP yace idan za'a yi zabe a bi doka. Doka tace za'a yi zabe ne wurin da aka yiwa mutane ragista ne. Ba'a taba yiwa sansanonin 'yan gudun hijira rajista ba. Doka bata san sansanonin ba. Zasu yadda a yi zabe a sansanonin 'yan gudun hijira idan majalisun tarayya suka canza dokar. A halin da ake ciki yanzu bai daceba, bai kamata ba a yi zabe a wuraren.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe da 'Yan Gudun Hijira - 3' 40"