Wasu shugabannin mata a Arewacin Najeriya na ganin cewar a na amfani da ‘yan siyasan Arewa don cimma wani buri, ganin yadda dubban mata da yara ke cikin halin ha’ula'i a yankin Arewa maso gabasa sanadiyyar rikice-rikicen kungiyar boko haram.
A cewar Hajia Hadiza Ningi, wada ake ma lakani da Hadiza ‘yar Ganye, tana ganin ba da gaske ake ba don ganin a kawo karshen wannan matsalolin na rashin tsaro a kasar baki daya ba. Tace a duk Najeriya babu yankin da ke da manya da yakai yankin arewa, amma ‘yayan su da jikoki da ake kashewa baji bagani, su gaskia basu ga alamar ana neman magance matsalara ba, don su mahukuntar suna babban birnin tarayya Abuja suna kwasar kudi.
Ta kara da cewar, ai Dr. Bawa Wase yace muna da karfin sojoji da zasu yaki kungiyar boko haram, amma anki daukan matakai da suka kamata. Alkalunmma na nuni da cewar mata da yara kanana su sukafi yawa a sannsanin ‘yan gudun hijira. Wannan batun na neman kulawa ta musamman a cewar Alh. Sa’adu Bello, jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA da ke kula da sannsanonin ‘yan gudun hijira a jihar ta Adamawa, yayi kira da gwamnatocin jihohin Arewa da ko ina a kasar, da su bada gudun mawa ga ‘yan gudun hijira da ke kwarara zuwa jihohinsu.
Shima babban jami’in hukumar Red Cross me kula da jihohin Arewa maso gabas, Alh. Aliyu Mekano, yayi Karin haske ga irin taimako da suke badawa, yace wannan ba wai taimako ne kawai na bangare dayaba, wannan yashafi kowa musamman ma ‘yan siyasa yakamata su bada tasu gudun mawa don taimakama wadanda ke neman taimakon gaggawa.