Adamu yace duk wani mutumin Borno dake tunanen zabe yanzu ya nuna rashin imaninsa ga al'ummar jihar.
Abun dake gaban jihar ba batun zabe ba ne. Abun dake gaban jihar shi ne yaya za'a yi mutane su koma gidajensu. Abu na biyu shi ne kawo karshen rashin rayukan da jihar keyi. Ba batun zabe ya kamata jihar ta damu kanta dashi ba yanzu.
Adamu ya cigaba da cewa wasunsu suna gaf da fitowa yin zanga-zanga ta nuna cewa basa bukatar zabe a jihar gaba daya. Batun wai zaben tamkar 'yanci ne sai Adamu yace kundun tsarin mulkin kasar ya nuna a yi zaben domin walwalar jama'a ne. Mutumin da ya bar gidansa bai san yadda yake rayuwa ba ta yaya zai yi maganar zabe. Yace a tambayi mutanen dake gudun hijira. Menene bukatarsu? Shin su yi zabe ne ko su koma gidajensu.
Batun cewa za'a shiryawa wadanda suke gudun hijira akwatunan zabe inda suke Adamu yace a je a tambayesu. Abun dake gabansu ba maganar zabe ba ce . A'a maganar yadda zasu koma gidajensu ya dauke masu rai. Suuna son su je su zauna gidajensu domin idan babu natsuwa batun zabe ma bai taso ba. Idan babu lafiya babu abun da zai tabbata balantana mutum yayi sha'awar zabe.
Gwamnatin dake ci a jihar Borno ita ce ta damu da zabe domin ta cigaba da mulki. Ya zargi gwamnatin Borno da gazawa wurin ceto wuraren da 'yan Boko Haram suka mamaye. Yace gwamnatin Adamawa ta fitar da kudi tayi anfani da maharba , 'yan kato da gora da jami'an tsaro ta fatattaki kungiyar Boko Haram daga jihar amma Borno ta kasa yin haka.
Bayan sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Adamawa su maharban sun je jihar Borno amma gwamnatin jihar tayi watsi dasu. Da suka gaji da jira suka koma inda suka fito. Duk halin da za'a bi a samu lafiya a daukeshi.
Adamu yace mafita ita ce gwamnatin jiha da ta tarayya da su talakawan a fito a hada karfi da karfe a bar batun siyasa domin a kwato jihar daga 'yan Boko Haram. Dole a tashi a yaki 'yan Boko Haram wadanda ke kashe mutane ba bisa ka'ida ba.
Ga karin bayani.