Zabe Baya Kawo Canji Sai da Ilmantar da Mutane-Inji Farfasa Zalanga

INEC

Bisa ga nazari da masana kimiyar zamantakewar dan Adam keyi zabe baya kawo canji sai da ilmantar da jama'a

An ga zabuka da yawa a kasashen Afirka amma basu yi tasiri ba wurin inganta rayuwar mutane ko a Najeriya ko a kasashen Afirka gaba daya.

A Afirka tunda kasashen suka samu 'yancin kai bata canza zani ba. Mutane na nan cikin jahilci da talauci.

Akwai zabuka da kan kawo canji amma idan ana son a san tasirin da suka yi sai dai a dubi tarihin kasashen gaba daya da kuma wasu abubuwa dake gudana. Sai an yi hakan za'a san ko zaben zai kawo canji.

Na daya akwai rashin ilmantar da mutane. A Najeriya misali duk da irin arzikin da take dashi ta kasa ilmantar da mutane. Hanya mafi sauki da za'a iya cutar mutane a koina a duniya shi ne a ki ilmantar dasu. Mutane su kasa sanin 'yancinsu, su kuma kasa sanin banbancin hagu da dama a rayuwarsu. Akwai mutane da yawa haka ba wai basu da kwakwalwa ba ne a'a domin an kasa ilmantar dasu ne.

Na biyu shi ne barin mutane cikin talauci. Idan aka bar mutum cikin talauci ya zama kodayaushe maroki ne, to bashi da wata kyakyawar magana da zai yi lokacin siyasa da zabe saboda kullum zai zo yana rokon wani abu domin talauci yayi masa katutu. Kullum yana tunanen yadda zai rayu ne.

A duk kasashen duniya bisa ga bincike matalauta basa iya shiga zancen siyasa yadda ya kamata domin abincin da zasu ci shi ne ya damesu.

Abu na uku shi ne rashin rikon amana. Idan aka dubi tarihin Najeriya akwai rashin rikon amana. A addinan Musulunci da na Kirista rikon amana nada mahimmanci. Idan an zabi shugaba kudin jama'a da kayansu ana son a rikesu da amana. Ya kamata yayi anfani da kudin jama'a ya inganta rayuwarsu domin kasar ta cigaba. Amma idan an duba sosai babu wani damuwa da zancen rikon amana. Sabili da haka koda an yi zabe idan babu rikon amana ba zai kawo cigaba ba.

Zabe kurum ba zai kawo canji ba saidai idan akwai shugabanni adilai. Wani abu kuma da yake bata kasar shi ne karyar addini. A shekarar 1960 da kasar ta samu 'yanci masallatai da mijami'u nawa ne suke kasar? Limamai nawa ne a kasar? Fastoci nawa ne? Duk wadannan sun karu amma kuma babu tsoron Allah. Idan da ana addini da gaskiya bakon da ya shiga Najeriya ba sai an yi masa wa'azi ba. Zai gani cewa akwai gaskiya cikin kasar to amma babu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe Baya Kawo Canji Sai da Ilmantar da Mutane-Inji Farfasa Zalanga - 3' 45"