ZABEN2015: Zabe Ba Makawa, INEC ta Kure Maleji - Inji Buhari

Janar Muhammadu Buhari dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin laimar jam'iyar hamayya ta APC.

Daga masaukin sa a London, ta wayar talho Muhammadu Buhari ya amsa tambayoyin Aliyu Mustapha akan zaben Najeriya, da kama Shekau da rai, da ma yin amfani da na'urar zabe.

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar jam'iyar hamayya ta All Progressives Congress APC a takaice, Muhammadu Buhari ya isa birnin London kuma har ya gabatar da jawabin da aka dade ana jira a Chatham House, cibiyar nazarin harakokin kasa da kasa ta birnin London.

A cikin jawabin da yayi a Chatham House Muhammadu Buhari ya kara jaddada aniyar shi tare da kara tabbatar da cewa a shirye yake ya tsaya takara kuma ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya na shekarar dubu biyu da goma sha biyar wanda aka dage yi daga ranar goma sha hudu ga watan Afrilu zuwa ranar ishirin da takwas ga watan Maris.

Muhammadu Buhari ya isa cibiyar tare da wasu kusohin jam'iyar APC da suka rufa ma sa baya, daga cikin su akwai tsohon gwamnan jahar Lagos Ahmed Bola Tinubu da shugaban jam'iyar APC na kasar Najeriya John Odigie Oyegun da gwamnan jahar Rivers Rotimi Amaechi da gwamnan jahar Edo Adams Oshiomhole da kuma tsohon gwamnan jahar Ekiti Kayode Fayemi.

Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto, ya samu tattaunawa da Muhammadu Buhari ta wayar talho jim kadan kafin yayi jawabin sa a birnin London.

Aliyu Mustapha Sokoto ya yiwa Muhammadu Buhari tambayoyi da dama da suka hada da maganar da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan yayi cewa za'a kama Shekau da rai kafin zabe, da batun na'urar zaben da za'a yi amfani ta, da farko Aliyu Mustapha Sokoto ya tambayi Muhammadu Buhari, shin ya ma tabbata za'a yi zaben nan?

Your browser doesn’t support HTML5

Ta Bakin Buhari Akan Zabe, Kama Shekau da Rai da Kuma Na'urar Zabe - 3'14"