Professor Rufa'i Ahmed Alkali, mai baiwa shugaban Nigeria shawara akan harkokin siyasa, yace bai ga dalilin da zai sa ba za'a yi zabe a Nigeria ba.
Professor Alkali ya fadi haka ne bayan anyi masa tambayar akan cewa yan Nigeria suna shakar ko za'a yi zaben na kuwa? Yace tsarin mulkin Nigeria ya kaiyade ranakun daya kamta ayi zabe, kafin a mika mulki hannun wanda yaci zabe.
Professor Alkali yace in dai ba an canja tsarin mulkin Nigeria ba, ranar ashirin da tara ga watan Mayu idan Allah ya kai mu za'a rantsar da sabuwar gwamnati a Nigeria. A saboda haka, cewa ba za'a yi zabe ba, wannan bai taso ba.