ZABEN2015: INEC Zata Tabbatar An Gudanar da Zabe -inji Jega

Attahiru Jega shugaban INEC

Daya daga cikin shugabannin kungiyar dattawan arewa da ake kira NEF a takaice yace ba zasu zabi shugaban da ya kasa hana kasan kiyashin da ake yiwa 'yan arewa ba.

Paul Unongo yace babu ranar da ba'a kashe akalla mutane dari biyu a arewacin Najeriya kuma shugabannin yanzu sun kasa yin katabus. Mr. Unongo yana mayar da martani ne akan zargin da 'yan Niger Delta a karkashin shugabancin Edwin Clark suka yi cewa dattawan arewa na shirya yin magudin zabe tare da hadin kan INEC.

Mr Unongo ya cigaba da cewa komemene Janaral Buhari ya yiwa mutanensu da can lokacin da yayi mulkin soja su yafe masa domin yanzu yana bin tafarkin dimokradiya. Yace basa son su sake yin wani kuskure domin wahalar da suke sha yanzu ta isa. Ya zama wajibi su zabi wanda zai ji kokensu a harshen da yake ji.

Akan zargin cewa shugabannin arewa sun hada baki da Farfasa Jega shugaban INEC saboda su zabi Janaral Buhari sai Mr Unongo yace su basu yi ba. Karya ce. Su wadanda suka yi zargin sun san karye su keyi. Sun yi hakan ne su tsorata mutane su ki goyon bayan Janaral Buhari.

Sakataren jam'iyyar APA Samaila Umar Sifawa yace zargin 'yan Niger Delta din shagube ne kuma kamata yayi gwamnati ta dauki mataki a kai. Duk abun da suke shiryawa 'yan Najeriya suna jiransu domin kowa yana ji a jikinsa.

Shi ma Farfasa Jega yace zargin bashi da tushe. Yace su dai a INEC sun dauki alkawarin gudanar da zabe. Ba zasu bari lokacin zabe ya wuce hurumin da dokokin zabe suka tanada ba. Dole a yi zaben kafin ranar 29 ga watan Mayu, ranar da za'a rantsar da shugaban kasa.Kamata yayi an yi zabe akalla kwana 30 kafin ranar da za'a rantsar da shugaban kasa. Hukumar zata yi duk iyakacin kokarinta ta tabbata an gudanar da zaben.

Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABE 2015: INEC Zata Tabbatar An Gudanar da Zabe -inji Farfasa Jega - 3' 33"