Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: APC A Adamawa Na Zargin Gwamnatin PDP


Janar Buhari dan takarar shugabancin Najeriya.
Janar Buhari dan takarar shugabancin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan kama dan tsohon Gwamnan jihar Abdulaziz Nyako da EFCC tayi.

Babbar jam’iyar adawa a Najeriya, APC, ta yi zargin cewa ana amfani da karfin mulki wajen cafke mata yayanta a jihar Adamawa, da tuni jami’an hukumar EFCC ta yi awon gaba da dan tsohon gwamnan jihar Abdul’Aziz Nyako.

Wannan ma na zuwa ne,yayin da aka dage yanke hukuncin karar da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako ya shigar a babban kotun tarayya dake Yola, yanzu aka maida shari'ar Abuja.

Shi dai dan tsohon Gwamnan yana takarar kuejrar majalisar dattijai daga mazabar Adamawa ta tsakiya.

Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohi masu zafin siyasa a Najeriya, lamarin yasa masu lura da harkokin siyasa suke nazartar lamuran siyasar jihar saboda irin salon da yake dauka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG