An kammala shirin kwashe sojojin dake atisaye a dajin dake yankin Sarkin Pawan Jihar Neja.
Wannan yunkurin kwashe sojojin ya jefa al’ummar dake zaune a yankin cikin zullumi da tashin hankali saboda yadda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu ba babbaka a yankin.
Mutanen dake zaune a kauyen Zazzaga daya daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa sun ce kwashe sojojin zai jefasu cikin mawuyacin hali.
Mazauna garin Zazzaga da dama suka tofa albarkacin bakinsu akan batun. Garba Audu Sarkin Hausawan Zazzaga ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaban sojojin da su yiwa Allah su bar masu sojojin.
A cewarsu da zarar sojojin suka tashi dole ne su ma su tashi daga garin. Ya lissafa garuruwa goma a yankin da mutane suka fice daga cikinsu saboda fitinar ‘yan bindiga.
Shi ko Muhammad Mai Gyero Zazzaga kira ya yi ga ‘yan jarida su gabatar da rokonsu ga shugaban kasa da shugaban sojojin. Idan ba’a taimaka masu ba wajibi ne su bar garin.
Dan Majalisar Dattawa dake wakiltar gabashin jihar, Sanata David Umaru ya bayyana irin barnar da ‘yan bindigan suka yi a yankin a ‘yan kwanakin da suka gabata. Inji shi an kashe mutane fiye da 40 kuma barayi sun raba mutanen da kudade fiye da Nera miliyan goma a Zazzaga kawai. Haka ma an yi barnar amfanin gona tare da kona gidajen jama’a.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta yi shirin maye gurbin sojojin da wata gamayyar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga da Civil Defense, da ma wasu sojojin domin tabbatar da tsaro a yankin, a cewar Kanar M.K. Maikundi wanda yake ba gwamnan jihar shawara akan harkokin tsaro.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5