Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 15 a Harin Maiduguri


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Bayan wani hari da maharan Boko Haram suka kai a yankin Balle Shuwa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, rundunar sojin kasar ta tabbatar da mutuwar mutane sama da goma.

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 15 ciki har da soja guda, bayan da mayakan Boko Haram suka kai wani hari a yankunan Balle Shuwa da Alkaramti a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin Darektan yada labarai na rundunar “Operation Lafiya Dole” Brig. Gen. Onyema Nwachukwu, ce ta tabbatar da mutuwar mutanen a yau Litinin.

A baya rundunar ta musanta zargin cewa an kashe mutane da dama ciki har da soja.

Sanarwar har ila yau, ta ce dakarun na Najeriya sun yi nasarar kashe mayakan shida da wasu ‘yan kunar bakin wake bakwai.

Yadda Mayakan Suka Kai Harin

Shafin yanar gizon jaridar Daily Trust ya ruwaito Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) yana cewa an yi ta jin harbin bindiga da fashe-fashe a daren jiya Lahadi a yankunan na Bale Shuwa da Alkaramti.

Yankunan na da nisan tafiyar kilomita 20 daga Birnin Maiduguri, babban Birnin jihar ta Borno.

Kamfanin dillancin labaran na NAN ya ruwaito cewa, maharan sun ajiye ababan hawansu ne nesa kadan da wani shingen binciken jami’an tsaro, suka tunkari inda suka kai harin.

Rahotannin sun ce dakarun Najeriya sun yi ta arangama da maharan, wadanda suka rika ta da bama-bamai tare da yin harbin kan mai-uwa-da-wabi a cewar shafin yanar gizon Premium Times.

Wata majiya ta ce daga cikin wadanda suka mutu har da sojoji Najeriya yayin wannan hari.

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Harin Maiduguri

A halin da ake ci, Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da wadannan hare-hare da aka kai a yankin na Bale da ke wajen birnin Maiduguri.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin shugaban hukumar da ke gudanar da ayyukan jin-kai a majalisar, Mr. Yassine Gaba, ya ce hare-haren da ake kai wa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya na kara ta’azzara.

“Mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba suna wahala daga hare-hare daban daban a arewa maso gabashin Najeriya.” Gabi ya fada a cikin sanarwar.

Ya kara da cewa “Hare-haren bama-bamai, da kashe-kashe da satan mutane da sace kayan jama’a, na ci gaba da yin mummunan tasiri akan mata da yara da kuma maza a kullum, saboda haka, muna kira ga dukkanin bangarorin da ke fada da su kawo karshen wannan yaki a kuma mutunta ran dan Adama.”

Wannan hari na zuwa ne kasa da sa'o'i 48 da aka kai wani hari a yankin Muna Garage da ke wajen Maiduguri.

Rundunar sojin ta Najeriya ta sha fadin cewa ta ci karfin mayakan na Boko Haram.

Amma kuma karin hare-haren da ake samu na nuna akasin haka kamar yadda masu lura da al'amura ke cewa.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane kana ya raba miliyoyi da muhallansu a wasu yankunan da ke kusa da Tafkin Chadi.

Saurari hirar Ibrahim Ka'almasi Garba da wakilinmu Haruna Dauda Biu kan wannan hari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG