Shahararren kamfanin sadarwar yanar gizo Facebook, ya bayyana kudirin sa na kayatar da shafin sa da bangaren ‘Manema Aure’ shugaban kamfanin Mr. Mark Zuckerbeg, ne ya bayyana haka, kamfanin zai fadada hanyoyin kyautatama jama’a.
Mark, ya sanar da hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da injiniyoyi masu kirkirar manhajoji, a wani taron kara wa juna sani mai take F8, ya kara da cewar, damar zata kara hada mutane a fadin duniya, da niyyar samar da karuwar auratayya ta hanyar amfani da yanar gizo.
Domin kuwa akwai kimanin mutane milliyan dari biyu da suka bayyanar kansu a matsayin samari da ‘yan mata marasa aure a shafin su na facebook, wanda hakan ya nuna cewar akwai bukatar kamfanin yayi wani abu don ba mutane damar haduwa da masoya.
Kamfanin dai ya shahara wajen sadar da zumunci a yanar gizo, tun dai a shekarar 2004 yake ba jama'a dama a shafin su bayyana ko suna da aure ko kuma A'a..
Ya kuma kara da cewar, kamfanin na kokari wajen kirkirar bangaren soyayya da zata kai ga aure, da kuma la’akari da abubuwa da suka shafi bayanan sirri na mutane. Wanda wannan babbar damuwa ce ga mutane da suke amfani da shafukan neman aure. Ganin cewar kamfanin kwananna ya yi kokarin warware matsalar kare sirrin bayanan masu amfani da shafin.