Yayinda yake jawabi yace yadda sojojin Najeriya suka kwato duk garuruwan da 'yan Boko Haram suka mamaye a jihohin Borno, Yobe da Adamawa haka ma zasu kwato 'yan matan Chibok.
Namadi Sambo yace a jihar Adamawa 'yan Boko Haram sun cafke kananan hukumomi bakwai amma duk an sake kwatosu. A Borno kananan hukumomi 14 'yan ta'adan suka mamaye amma an kwato 13 saura daya tak, wato Gwozah. Yace ita ma za'a kwatota. Yace haka ma zasu kubutar da 'yan matan Chibok da yaddar Ubangiji..
Mataimakin shugaban ya alakanta tafiyar hawainiya da aikin babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri keyi da rashin tsaro da kungiyar Boko Haram ta haddasa. Yace a wajen Bauchi 'yan ta'adan sun sace turawa guda biyar dake aikin hanyar. A yankin Yobe da Borno hakan ma ya faru. Sabili da sace ma'aikatan da 'yan Boko Haram su keyi 'yan kwangilar basa iya aikinsu. Yace idan ba haka ba da tuni an gama gina hanyar.
Dangane da batun zabukan da za'a yi mataimakin shugaban ya musanta batun cewa PDP tana tsoron yin anfani da naurar tantance masu jefa kuri'a. Yace "bari inyiwa 'yan Najeriya da duniya gaba daya bayani PDP bata da tsoron komai a wannan zaben da za'a yi. Kowane lungun kasar akwai PDP" Yace saboda haka tsoron me PDP za ta ji. Yace abun da suke cewa shi ne a yi adalci a zaben.
Ya kara da cewa a tabbatar kowa ya samu katin zabe. Dangane da naurar da za'a yi anfani da ita yace an samu miskila da ita a wasu wurare. Sabili da haka a bi dokar kasa kan abun da tace dangane da yin anfani da naurori.
Ga rahoton Mahumud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5