Shugabannin Fulani daga kananan hukumomi 21 da ke jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya, sun yi Allah wadai da hare-haren da ‘yan fashin daji suke kai wa a yankunan jihar da kewaye.
Jagororin Fulanin sun bayyana hakan ne yayin ziyarar da suka kai fadar gwamnatin jihar a Birnin Kebbi, don jajantawa hukumominta bisa sace daliban sakandaren Yauri a makon da ya gabata
A makon da ya gabata ‘yan bindiga suka shiga makarantar sakandare ta tarraya da ke Yauri suka yi awon gaba da dalibai da dama da malamansu, lamarin da ya sa gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ayyana cewa zai jagoranci wata gayya da za ta shiga daji don kubutar da daliban.
“Dukkan mun taru a nan ne, don mu nuna goyon bayanmu ga gwamnna Bagudu sannan mu bayyana shirinmu na shiga wannan yaki na ceto daliban.” Shugaban Fulanin jihar ta Kebbi Alhaji Bello Aliyu Gotomo ya fadawa gwamnan.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin ziyarar da suka kai wa gwamnan a farkon makon nan kamar yadda wata sanarwa da gwamnatin ta fitar dauke da sa hannun mai bai wa gwamna shawara kan harkara yada labarai Yahaya Sarki.
A lokuta da dama, akan zargin Fulani ne da kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohin da ke arewa maso yammacin Najeriya, amma Gotomo ya ce su ba sa goyon bayan wannan aika-aika.
“Ba ma goyon bayan fashin daji ko kadan, ko wa ya shafa, mu ma makiyanmu ne, a shirye muke mu hada kai da jami’an tsaro don a murkushe su.” Gotomo ya kara da cewa.
A cewarsa, ‘yan bindigar, sun saka al’umar Fulani cikin mawuyacin hali, ta hanyar sace masu shanu sannan sun hana manoma zuwa gonakinsu.
Yayin nasa jawabin Gwamna Bagudu wanda ya samu wakilicin mai ba shi shawara kan harkar tsaro Manjo Janar Garba Rabiu Kamba mai ritaya, ya kwatanta ziyarar shugabannin Fulanin a matsayin abin kwarin gwiwa a kokarin da ake yi na kawo karshen ‘yan fashin dajin a jihar.
Kazalika ya kara jaddada aniyarsa ta jagorantar gayya don yaki da maharani, “wadanda suke kuntatawa rayuwar al’umar jihar ta Kebbi.