Ya ce ‘’idan ba mu sami kwato makaman ba, babu wanda zai sami sukuni a wannan kauye, saboda za’a iya amfani da makaman wajen kashe mutane da aikata mugayen laifuka kuma ba zamu yadda da hakan ta faru ba.’’
Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya ce akwai wasu mutane 40 da rundunar ke da bayanai a kan su, wadanda kuma ya gargadesu, saboda ya ce ya san abin da suka aikata, da kuma abinda suke shirin yi, domin haka doka za ta yi aikinta a kansu.
Matalolin da mazauna yankin ke fuskanta sun hada da kisan sari-ka-noke, lalata amfanin gona, kisan dabbobi ta hanyar sanya musu guba, barin yara kanana suna kiwo a gonaki, kai hare-hare da ramuwar gayya da sauransu.
Shugaban kungiyar raya al’ummar Butura, a karamar hukumar Bokkos, Philip Julson, ya ce daya daga cikin sinadiran samar da zaman lafiya a yankin shi ne fadawa juna gaskiya kan abin da ke faruwa da kuma tsayuwa kan gaskiyar.
To sai dai a ra'ayin Malam Sale Yusuf Adam, shugaban kungiyar Fulani ta Gan-Allah a karamar hukumar Bokkos, yin adalci ne muhimmin abin da zai samar musu da zaman lafiya a yankin.
A cikin kwankin nan rundunar Operation Safe Haven ta kama bata-gari da dama da suka hada da masu garkuwa da mutane, masu sarrafa makamai da masu kisan ba gaira ba dalili, wadanda rundunar tace dole sai sarakuna da ardo-ardo sun sanya ido kan wadanda ke shigowa yankinsu daga wasu wurare, saboda idan aka sami wani rikici, su ma shugabannin ba za su tsere wa fushin hukuma ba.
Saurari sautin rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5