Za Mu Kalubanci Sakamakon Zaben Bassa/Jos Ta Arewa A Kotu - Dan Takarar PRP

Your browser doesn’t support HTML5

Zamu kalubanci sakamokon zaben da ya gudana a yakin Jos ta Arewa-- Dan takarar jam'iyyar PRP Muhammad Adam Alkali.mp4

A ranar Lahadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Musa Avia Agah  a matsayin wanda ya lashe zaben.

Akwai abubuwan da aka yi wadanda suka saba dokokin kasa, sun saba dokokin hukumar zaben kasa da kuma 'yancin dan adam, don haka za mu kalubalenci hakkin al’ummar wannan mazaba a gaban kuliya

ABUJA, NIGERIA - Biyo bayan zaben maye gurbin dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar mazaben Jos ta arewa da Bassa a jihar Filato da ya gudana a ranar Asabar, dan takarar jam’iyyar PRP Muhammad Adam Alkali wanda jam’iyyarsa ta zo ta biyu da kuri’u dubu 37,757 ya bayyana cewa bai gamsu da sakamakon zaben ba.

A cewar Muhammad Alkali akwai wasu rumfan zabe da ba’a kawo sakamakonsu ba akan lokaci kuma ko da sakamakon ya iso sai aka bayyana cewa jam’iyyar PDP ita ke kan gaba.

A cewar Muhammad Alkali, akwai abubuwan da aka yi wadanda suka saba dokokin kasa da na hukumar zaben ta kasa wato INEC da kuma yancin dan’ Adam.

Muhammad ya ce jam’iyyarsa za ta kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotu don nemawa al’ummar wannan mazaba hakokkinsu.

Ya na mai cewa ‘’akwai abubuwan da aka yi wadanda suka saba dokokin kasa, sun saba dokokin hukumar zaben kasa da kuma 'yancin dan adam, don haka zamu kalubalenci hakkin al’ummar wannan mazaba a gaban kuliya’'

A ranar Lahadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Musa Avia Agah a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wata rumfar zabe

Da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi, jami’in zabe na hukumar INEC, Yinka Oyerinde, ya ce Musa Agah na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 40 da 343 inda ya kada abokin hamayyarsa, Gwani Muhammed Adam Alkali na jam’iyyar Peoples Redemption Party wato PRP da ya samu jimillar kuri’u dubu 37 da 757 yayin da Abbey Aku na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 26 da 111.

Jam’iyyun siyasa 11 ne suka fafata a zaben maye gurbi na ranar 26 ga watan Fabrairu domin cike gurbin da Haruna Maitalla na jam’iyyar APC wanda ya rasu a wani hatsarin mota a watan Afrilun shekarar 2021 da ta gabata ya bari.

Saurari karin bayani cikin wannan sauti

Your browser doesn’t support HTML5

DAN TAKARAR JAM'IYYAR PRP Gwani Muhammad Alkali