Za Mu Girke Karin Jami'an Tsaro A Kudancin Jihar Maradi - Bazoum

A yayin rangadin da ya fara a rasar Lahadi a jihar Maradi, shugban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bayyana shirin kara girke jami’an tsaro da karin kayan aiki a ci gaba da neman hanyoyin murkushe ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi al’umar yankin dake samun dubban ‘yan gudun hijira daga Najeriya.

Karfafawa jami’an tsaro gwiwa da jaddadawa al’uma goyon baya a wannan lokaci da ‘yan bindiga suka addabi mazaunan garuruwan kudancin jihar Maradi sakamakon tabarbarewar sha’anin tsaro a wasu jihohin arewacin Najeriya ya sa shugaban kasar Nijar kai ziyara a kauyen Gabi na gundumar Madarounfa.

Shugaba Mohamed Bazoum ya jaddadawa talakkawadamuwarsa a game da halin da suke ciki.

Shekaru a kalla uku kenan da aka shiga zaman dar-dar a gundumar Madarounfa kuma shine karon farko da shugaban kasa ke tattaki zuwa wannan karkara domin jajantawa jama’a game da halin da suka tsinci kansu ciki.

Mohamed Bazoum dake samun danne gargada daga ministan cikin gida Alkache Alhada da takwaransa na tsaron kasaAlkassoum Indatouda manyan hafsoshiin sojan kasar ya jagoranci taron kwamitin tsaro na kasa a Maradi saboda haka ya yanke shawarar kara tsaurara matakan tsaro ajihar.

Shugaban ya ziyarci barikin sojan shiyya ta shida dake Maradi ya na mai jinjina wa abinda ya kira jajircewarsu akan aiki .

A ranar Litinin wuni na biyu na karshe a wannan rangadi tawagar shugaban za ta isa garin Dan Kano na gundumar Gidan Roumji domin baiwa jama’agoyon baya sakamakon azabar da suke fuskanta daga wajen barayin shanu da masu satar mutane don neman kudin fansa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Za Mu Girke Karin Jami'an Tsaro A Kudancin Jihar Maradi - Bazoum