Shugaban hukumar kiyaye haddura na Najeriya, Boboye Oyeyemi, yace hukumarsa zata horar da jami’ai, na hukumar kasuwancin jiragen ruwa kan yadda lasisi da rajistan manyan motoci yake domin gudanar da wannan aikin yadda ya dace.
Ya kara da cewa hukumar zata duba lafiyar manyan motocin domin suke jigilar kashi tasa’in cikin dari na kayan masarufi a dukkan fadin Najeriya.
Idan wannan yarjejeniya ta fara aiki gadan gadan inji shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Malam Hassan Bello, za a ga cewa duk inda suke babu irin kazantar da aka saba gani kuma za a samarda mahimman abubuwan da suka dace kuma tuni wasu Gwamnoni sun fara yunkurowa.
Zaa yi amfani da naurori domin ganin duk inda manyan motoci suke da daukar matakin da ya dace idan suka tsaya a inda bai dace ba. Makon gobe duk masu ruwa da tsaki na wannan tashoshi zasuyi taro a Legas, domin Karin bayani akan wannan aikin dake da nasaba da raya tattalin arziki da zamanantar da harkokin mayan motoci.
Your browser doesn’t support HTML5