Za'a Yankewa Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Shugaban Amurka Hukunci

Paul Manafort

A yau Laraba ake sa ran yankewa tsohon shugaban yakin neman zaben shugaban Amurka Paul Manafort hukuci , a kotun tarayya dake nan Gundumar Kwalambiya, akan laifufuka guda biyu.

Alkali Amy Berman Jackson, tana iya yanke mishi hukuncin gidan kaso na tsawon shekaru 10.

A makon da ya gabata wani alkali ya yanke mishi hukuncin gida yari na tsawon watanni 47 akan laifin kin biyan haraji da zanba cikin aminci ga banki.

Ya dai rage ga alkali Jackson ko ta sa shi yayi wa’adin shin a gidan yari a lokaci guda, ko kuma ta ce zai fara wa’adin sabon zaman bayan ya kammala zaman laifinshi na farko.

Alkali Jackson ta taba yanke ma Manafort hukunci a shekarar da ta gabata, na daurin talala bisa laifin bada shaidar zur.