Za A Tuhumi Jami’an Lafiya Takwas Kan Mutuwar Maradona

Diego Maradona

Fitaccen dan wasan na kasar Argentina ya kwashe shekaru da dama yana fama da matsalar amfani da hodar iblis da shan barasa. A watan Nuwambar 2020 Maradona ya mutu.

Za a gurfanar da wasu jami’an lafiya takwas a gaban kotu kan zargin laifin sakaci da suka yi wanda ya yi sanadin mutuwar shahararren dan wasan kwallon kafa Diego Maradona yayin da ake masa magani bayan wata tiyata da aka yi masa.

A ranar Laraba ne wani alkali ya ba da umarnin a gudanar da shari’ar kan zargin kisan kai da mutanen takwas din suka yi, wadanda suka hada da likitan iyalin Maradona da ma’aikatan jinya, bisa hujjar cewa sun nuna sakaci a kulawar da suka masa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa a watan Nuwamban 2020.

Ya zuwa yanzu dai ba a saka ranar da za a fara shari’ar ba.

Maradona ya mutu yana da shekaru 60 a lokacin da yake murmurewa daga wata tiyatar da aka yi masa a kwakwalwa saboda matsalar daskarewar jini da yake fama da ita.

Fitaccen dan wasan na kasar Argentina ya kwashe shekaru da dama yana fama da matsalar amfani da hodar iblis da shan barasa.

An gano cewa ya mutu ne sakamakon matsalar bugun zuciya.