Gwamnatin Najeriya ta baiwa ‘yan kasar tabbacin cewa za’a yi adalci a shari’ar da ake yi wa jagoran kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Ministan shari’a na kasar Abubakar malami ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a sha’anin watsa labarai Dr. Umar Jibrilu Gwandu ya fitar, inda ya ke cewa za’a yi hakan ne bisa tsarin ba shi damar kare kan sa da ke kunshe a kundin tsarin mulki.
Ministan ya kuma yabawa matakin kungiyar nan ta ‘yan kabilar Igbo, wato ‘Ohanaeze Ndigbo’ da ke kudu maso gabashin Najeriya, akan hada ayarin kwararrun lauyoyi da masana shari’a, da za su sanya ido kan zaman shari’ar ta Nnamdi Kanu.
Ya ce wannan matakin na kungiyar, ya dada tabbatar da amincewar su na kasancewa ‘yan Najeriya, da kuma matsayar su na bin dokar kasa, a yayin da kuma suke bayyanawa karara cewa ba sa kalubalantar gurfanar da Nnamdi Kanu da aka yi a gaban kotu.
Ya kara da cewa “kungiyar ta Ohanaeze ta kuma nuna karara cewa ba ta tare da haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB, sa’adda ta ce ba ta goyon bayan ko wane irin nau’i na tashin hankali a yayin gabatar wata bukata ko wani korafi.”
Haka kuma Ministan ya bayyana cewa kiran da kungiyar ta yi wa matasan yankin da su kasance masu bin doka da oda, su kuma yi kokari mallakar katin zabe domin ba da ta su gudummuwa ga ci gaban kasa, ya nuna cewa matakin na Ohanaeze yayi daidai da tanadin doka, kuma abin yabawa ne.
Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Igbo, Biafra, Biyafara, DSS, IPOB, Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
To sai dai kuma Ministan ya bayyana fatar cewa tawagar masana shari’ar da kungiyar ta kafa, za su sanya ido kan shari’ar ne da zuciya daya, su kuma fuskanci tanadin doka a daukaci zaman shari’ar, ta yadda za su iya sadar da hukuncin da duk kotu ta yanke zuwa ga mutanensu, da ma daukacin ‘yan Najeriya baki daya.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, ta kuduri aniyar tsare bin doka da oda, akan haka ta yi niyyar tabbatar da adalci a shari’ar ta Nnamdi Kanu kamar yadda doka ta tanada, ko da wannan tawagar lauyoyin ko babu.
A ranar 26 ga wannan watan ne dai ake sa ran komawa zaman shari’ar ta Nnamdi Kanu gadan-gadan a babbar kotun tarayya a Abuja.
Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
Your browser doesn’t support HTML5
VOA60 AFIRKA:An Kama Shugaban Kungiyar ‘Yan Awaren Biafra Nnamdi Kanu
Your browser doesn’t support HTML5