Za A Samu Matsanancin Karancin Abinci A Sudan Ta Kudu

Displaced people draw water from a hole dug in the ground, in the United Nations camp for displaced people in the capital Juba, South Sudan, Jan. 19, 2016.

Majilisar Dinkin Duniya tayi gargadi a jiya litini cewa za a samu matsanancin karancin abinci a kasar Sudan ta Kudu, wanda hakan zai tura dubun dubatar ‘yan kasar cikin halin kaka ni kayi na rashi abinci musammam ma fafaren hula.

Wannan gargadin dai ya biyo bayan sakamakon rahoton da majilisar ta samu ne wanda ya bayyana cewa an kiyasta a kalla mutanen da yawan su ya kai mililan 2.8, wanda wannan yana nufin adadin kashi 23 kenan na mutanen kasar zasu fuskanci wannan iftilain tsakanin cikin watan Janairu da na Mayun wannan shekarar.

Rahoton yaci gaba da cewa yawancin wadannan mutanen da wannan lamari zai rutsa dasu ko suna zaune ne a yankin Unity Jonglei da kuma can samar yankin kogin Nilu, wannan adadin kuma yakai na kashi 57 ne na ‘yan rabbana ka wadata mu.

Majalisar Dinkin Duniya tace wani abin shakkun kuma shine ana hasashen wannan lamarin ya kara muni tsakanin watan Afirilu zuwa watan Juli, lokacin da abinci zaiyi kasa kwarai da gaske kana yunwa ta kara tsananta.