A cikin gida, kafofin yada labarai da gwamnati kadai take iya juya akalarsu, suna bayyana matashin shugaban kasar a zaman wani jarumin dake kare diyaucin kasar daga kokarin nuna fin karfi na Amurka da Koriya Ta Kudu ko KTK.
Kafofin labaran sun bayyana harba rokar da aka yi jiya lahadi a zaman wani gagarumin ci gaban fasaha na kasar dake samun ci gaba sosai, abinda ya kara ma al’ummar KTA yin alfahari da kasarsu.
Cibiyar hadin guiwa ta kula da ayyukan sararin samaniya ta Amurka ta ce harba rokar da KTA ta yi jiya lahadi, ta kaddamar da wasu abubuwa guda biyu masu shawagi a sararin samaniya, amma ba a san ko suna aikewa da sakonni ba.
Har yau ba a ga alamar wani sako na fita daga wani tauraron dan Adam da KTA ta cilla a shekarar 2012 ba, wanda har yanzu yana kewaya duniya kowane minti 95.