Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Afirka bata manta da 'yan Burundi ba - AU


Taron shugabannin Afirka
Taron shugabannin Afirka

Mataimakin shugaban majalisar zartaswar tarayyar Afrika da ake kira AU a takaice ya ce hukumar ba ta manta da ‘yan Burundi ba a taron da aka yi makon da ya gabata saboda kasa tura dakarun wanzar da zaman lafiya kasar, sabanin ikirarin da ‘yan adawar Burundi su ka yi.

Shugaban ‘yan jam’iyyar adawa ta Front for Democracy a Bururndi da ke gudun hijira yanzu haka, ya zargi tarayyar ta Afrika da kasashen duniya da juyawa Burundi baya da su ka yi, yayin da gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza ke kashe mutane.

An fara tashin hankali a kasar ne lokacin da shugaba Nkurunziza ya so yati tazarce, domin neman wa’adi na uku kan mulki, abinda ya sabawa tsarin mulkin kasar wanda ya kayyade yin shugabanci sau biyu .

Mataimakin shugaban kungiyar ta AU Erastus Mwencha ya ce shugabannan Afrika sun yi cikakkiyar ganawa game Burundi kuma sun yanke shawarar za’a bayar da dama domin a ga kamun ruwan tattaunawar neman warware wannan daurin gwarmai tsakanin bangarorin kafin su tura dakarun wanzar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG