Za A Maye Takardar Kudin Cfa Da Sabuwar Takardar Kudin ECO

Shugaba Alassan Ouattara

Masana na ci gaba da bayyana matsayinsu akan kudirin Shugaban Kasar Cote d’ivoire, Alassan Ouattara, na kammala shirin maye takardar kudin Cfa da sabuwar takardar Kudaden ECO a kasashe 8 na yammacin Afrika renon Faransa, daga tsakiyar shekarar 2020.

A karkashin wannan kudiri, shugaba Ouattara ya bayyana wa taron manema labarai na hadin guiwa da Emmanuel Macron na Faransa, kasashe 8 na yammacin Afrika renon Faransa mambobin kungiyar Uemoa sun yanke shawarar jingine takardar kudi ta Cfa daga watan Yulin badi domin soma amfani da takardar ECO.

Wannan shine ainihin shirin da kungiyar ECOWAS ke jagorantar da samarda ita, matakin da masanan tattalin arziki irinsu Dr Soly Abdoulaye ke ganinsa tamkar wani zagon kasa ne.

Wannan sabon tsarin da shugaban na cote d’ivoire ke shirin shimfidawa na iya zama barazna ga sha’anin tattalin arzikin nahiyar Afrika baki daya, inji Abdoul kader Issa Ousman na kungiyar masu kyamar takardar kudin cfa.

Yace, wannan wani mataki ne da zai iya dagula aiyukan fitarda kayan sayarwa daga Afrika zuwa sassan duniya, saboda haka idan matakin canzawa Cfa suna ya tabbata, tattalin arzikin kasar na cikin mugun hadari.

A Faransa ne ake sa ran kafa injinan buga takardar kudin na ECO, sannan ita ce za ta kasance uwar daki ga kasashen dake karkashin wannan tsari, lamarin da ya sa kasashen da britaniya ta yiwa mulkin mallaka suka fara nisanta kansu daga wannan yunkuri inji masana.

Jami’in fafitika Abdou ELH.Idi na kungiyar FSCN na kallon wannan tsari a matsayin wata hanyar raba kan kasashen Afrika ta yamma da nufin cimma wata manufa.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Maye Takardar Kudin Cfa Da Sabuwar Takardar Kudin ECO