Za A Maye Gurbin Rundunar SARS:AIG

Shugaban 'Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya yi karin haske kan soke rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi da makami wato “Special Anti Robbery Squad” ko SARS a takaice, wacce yanzu ana tsara kafa wata sabuwar runduna da zata maye gurbinta.

Wannan ya biyo bayan jerin zanga zanga da wasu gungun kungiyoyin
fararen hula su ka yi ta gudanarwa a Abuja da wasu manyan biranen
kasar don ganin an soke wannan runduna bisa zarge zargen yin
karan tsaye da akewa jami'anta.

Shugaban ‘yan sandan Najeriyar ya ce daga yanzu za a samar da wani
dandali inda shugabannin ‘yan sandan zasu yi aiki kafada da kafada da
jama'a a dukkannin matakai don sa ido a kan ayyukan ‘yan sandan.

Sai dai wannan mataki na rundunar ‘yan sandan bai yiwa wasu ‘yan kasar dadi ba, domin a yayin da ake tsakiyar wannan zanga zangar ne kuma
majalisar matasan arewa ta aikewa da shugaba Buhari wata doguwar
wasikar neman kin amincewa da soke rundunar ta SARS, tana mai cewa
hakan ka iya kara tabarbarar da yanayin tsaro a yankin arewacin kasar.

Shugaban majalisar Zaidu Ayuba Alhaji, ya shaidawa Muryar Amurka cewa
irin rawar da rundunar SARS ke takawa a shiyyoyin Arewa maso gabas da
Arewa maso yamma na tabbatar da tsaro, lalle soketa zai haifar da gibi
babba.

Shima masanin tsaro Group captain Sadik Garba Shehu, ya ce da maimakon
soke rundunar garambawul ya kamata a yi mata, tunda ai mutanen da suke
aikin har yanzu su ‘yan sanda ne.

Ga dai rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

IGP NA SHIRIN RUSA RUNDUNAR 'YAN SANDA TA SARSA