Za a Kama Duk Malamin Da Ya Kawo Almajirai Kaduna- Elrufa'i

Wadanda 'yan sanda suka ceto a wata makarantar Islamiya a Kaduna.

Maganar dakatar da almajiranci na ci gaba da daukar hankali a jihar Kaduna, saboda gwamnati ta dage kan cewa, za a kama duk malamin da ya kawo almajirai. jihar.

Tuni dai gwamnatin jahar Kaduna ta kafa kwamiti na masamman don tattara almajirai da kuma maida su gidajen iyayen su wanda tuni ya dibe daruruwan almajirai ciki har da na makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Gwamnan Jahar, Malam Nasiru Ahmed El-rufai wanda ke amsa tambayoyin manema labaru a wajen wani taro a Kaduna, ya ce gwamnati na nan kan matsayin ta cewa ta hana Almajiranci a jahar baki daya.

Yara a makarantar allo

Bisa ga cewar gwamnan, almajiranci wata hanya ce ta taka hakkin kananan yara. Yace hakki ne kan iyaye su lura da 'ya'yansu, su ilimantar da su ba su ba wani ya lura da su ba, sabili da haka idan aka sami wani yana shigo da yara aljamiranci a cikin Kaduna, za a kama shi a kuma maida yaran wajen iyayen su.

Karin bayani akan: Nasiru Ahmed El-rufai, Nigeria, da Najeriya.

Gwamna Nasiru Ahmed El-rufai ya ce," Bara ne ba mu so, domin bara ba addini ba ne, bara ba musulunci ba ne, bara ba ya cikin al'adun mu"

Gwamnan ya kara da cewa, masu wannan ra'ayin su na cewa, ana hana bara ne domin ba a son addini, sai dai ya ce su ma sun yi karatun kur'ani amma ba su yi bara ba, kuma zai iya fitar da mutane dari a garin Kaduna da suka sauke kura'ani amma ba su taba yin bara ba.

Usman Mohammed, wani dan gwaggwarmaya kan tsarin almajiranci

Wannan jadada matsaya kan dakatar da Almajiranci da gwamnan jahar Kaduna ya yi da kan shi, ya jawo hankalin malaman makarantun Tsangaya na jahar Kaduna wadanda su ka ce ba haka su ka yi da gwamnatin ba.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Gwani Suleman Idris Mai-zube shugaban wannan kungiyar malaman makarantar Tsangaya na jihar ya bayyana cewa, basu ga yadda ake take hakkin yara a tsarin makarantun Tsangaya ba. Bisa ga cewar shi, duk lokacin da mutum ba ya son wani abu, ya kan nemi hanyar da zai bakanta shi domin matsayin shi ya sami karbuwa.

shawarar-mai-alfarma-sarkin-musulmi-ta-karatu-ba-bara-na-dada-karbuwa

an-fara-musayar-yawu-kan-batun-jigilar-almajirai

gwamnatin-sokoto-ta-ce-ba-za-ta-kori-almajiran-jihar-ba

Shugaban Malaman makarantun Tsangayan ya ce, yaran da suka yi karatu a makarantun Tsangaya su kan fita dabam da sauran yara, domin banda samun ilimi, su na nuna ladabi da biyayya.

Yaran tsangaya da barace barace a Nijar

Tun bayan kaddamar da kwamitin maida almajirai garuruwan su a jahar Kaduna dai aka fara wasan buya tsakanin almajirai da kuma 'ya'yan kwamitin amma duk da haka kwamitin ya kama Almajirai da dama.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Za a Kama Duk Malamin Da Ya Kawo Almajirai Kaduna- Elrufa'i-3:10"