Batun jigilar Almajirai a tsakanin gwamnocin arewacin najeriya na ci gaba da kara tsamin dangantaka tsakanin mamallaka makarantun tsangayu a yankin Alarammomi a Kano da kuma gwamnatin jihar.
Gwamnatin Kano ce dai ta fara jigilar almajiran zuwa jihohin Jigawa da Kaduna su kimanin dubu 2, a wani bangare na yunkurin ta na hade tsarin karatun allo dana book.
Matakin dai ya haifar da cece-kuce tsakanin gwamnonin Kano da Kaduna a hannu guda, inda a daya hannun dangantaka ta so tayi tsami tsakanin gwamnatin Jigawa da ta Kano.
A kwanakin baya dai gwamnan Kaduna Nasir Elrufa’I yayi zargin takwaransa na Kano da kara alkaluman masu dauke da cutar Korona saboda almajiran da Kanon ta mayar zuwa Kaduna.
Yanzu haka dai makamanciyar waccan takaddama na wanzuwa tsakanin Hafizan Alkur’ani a jihar Kano da gwamnatin jihar, domin sun bayyana matakin korar almajiran da cewa wani yunkuri ne na tozarta tsarin koyon karatun alqur’ani.
Gwani Lawi Gwani Danzarga shine shugaban kungiyar mahaddata alqur’ani ta jihar Kano kuma ya sheda wa Muryar Amurka cewa "mu muna da karancin gata, ana yin abu ba tare da an shawarce mu ba."
"Me yasa ba za ayi wa karasun alkur'ani gata ba, a gyara tsarin."
Sai dai kwamishinan ilimi na Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Kiru na cewa "sun mayar da harkar almajiranci kamar kasuwanci."
"Shi yasa kake ta jin kara akan batun. Kwannakin baya gwamnati ta ce a kawo almajirai zuwa ma'aikatar harkokin ilimi amma duk suka ki kawo daliban nasu saboda sun san cewa idan suka kai su, to kasuwancinsu zai tafi."
Dangane da fahimtar da wasu keyi cewa, matakin na gwamnati, tamkar yunkuri ne na korar baki daga Jihar, lamarin da masu kula da lamura ke cewa, da karbar bakin ne kanon ta bunkasa.
Tuni dai gwamnonin Borno da Yobe da kuma Sokoto suka ayyana cewa, babu wani almajiri da zasu kora daga jihohinsu, yayin da gwamnan Jigawa yace sai bayan annobar korona zai nazarin matakin daya dace.
Saurari rahoton a sauti.
Facebook Forum