Za A Kafa Rundunar JTF A Zamfara

ZAMFARA: Jirgin yaki

Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi jihar, sakamon ci gaba da kai hare hare da garkuwa da jama'a da ake fuskanta.

Duk da rundunonin soji tare da jiragen yaki da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tura a jihar Zamfara, ana ci gaba da samun yawaitar ayyuka ‘yan bindiga, kama daga kai hare-hare, da kisan jama’a, har ma da satar mutane domin karbar kudin fansa, wanda a yanzu ya zama ruwan dare a jihar.

To sai dai gwamnan jihar Abdul aziz Yari Abubakar, ya ta’allaka wannan yanayin da rashin iya game dukkan yankunan jihar a lokaci daya da jami’an tsaron, duk kuwa da yawan da suke da shi.

A kan haka ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro a Gusau babban birnin jihar, Gwamna Yari ya bada sanarwar matsayar da aka cimma ta kafa rundunar hadin gwiwa da farar hula, wato “Civilian JTF” a turance, a karkashin jagorancin hukumomin tsaro a jihar.

Tuni da aka yi haramar samar da dokar kafa sabon tsarin a majalisar dokokin jihar, inda za’a dauki matasa kusan 8,500 da za’a horar da su, tare kuma da biyansu alawus na naira 15,000 a kowane wata, kari ga alkawarin bada tukuicin naira miliyan daya ga duk wanda ya kama dan ta’adda mai bindigar AK47.

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

Your browser doesn’t support HTML5

Za a kafa rundunar JTF a Zamfara-3:13"