Wata kungiyar kasar Jamus mai suna GIZ da hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa ta Nijar da jami'an tsaro da kungiyoyin farar hulla da yan jarida, na gudanar da taro gameda yaki da cin hanci da rashawa a kan iyakokin kasar da sauran kasashen ECOWAS
Birnin Nkonni, Niger —
Ana can ana gudanar da wani zaman taro na kwanaki 2 a garin Birni N'Konni da ya hada shugabanin sufuri da jami'an tsaro da ke iyakokin jamhuriyar Nijar da shugabannin jama'a a karkashin laimar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jamhuriyar Nijar da tallafin kungiyar GIZ ta kasar Jamus.
Makasudin taron shi ne yaki da cin hancin da rashawa a iyakokin kasar da ma yankin kasashen ECOWAS ko CEDEAO inji mai kula da rigakafin aikata laifi a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jamhuriyar Nijer.
Shin wace gudunmawa ce jami'an tsaro da a ke ganin suke da hannu dumu - dumu a wannan mugunyar dabi'a za su ce game da karbar cin hanci da rashawa a iyakokin kasar? Wannan ita ce tambayar da wakilin Muryar Amurka ya yi wa daya daga cikin su dake halartar wannan taron, wanda kuma bayyana ra'ayinsa da kuma hanzarinsu a bangaren tsaron.
A nasu bangaren, masu jigilar fasinja daga Nijar zuwa Najeriya sun ce dole ne ya sa barin yin lodi da motoci masu lambar Nijar zuwa Najeriya.
Ita dai wannan bakar dabi'a ta cin hanci da rashawa, ta dade tana hana habbakar tattalen arzikin kasashen yammacin Nahiyar Afurka, hasali ma, ana gudanar da irin wadanan tarukan, amma kamar ana sakiya ne kai na kaba.
Saurari cikakken rahoton Harouna Bako:
Your browser doesn’t support HTML5