Za'a Iya Shawo Kan Matsalar Tsaro A Najeriya Idan An Sa Kishin Kasa Da Fahimta - IBB

  • Murtala Sanyinna
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soji Janar Ibrahim Badmasi Babangida, ya bayyana yakinin cewa za’a iya shawo kan matsalar tsaro da ke addabar dukkan sassan kasar ne kadai, idan aka sami kishin kasa da fahimta tsakanin gwamnati da ‘yan kasa.

A yayin da yake mika sakon barka da sallah ga ‘yan Najeriya a wata kebantacciyar tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Janar Ibrahim Babangida ya ce wannan yanayi na kalubalen tsaro da Najeriya ke ciki ba bakon al’amari ba ne, domin kuwa ya shafi kasashe da dama, a lokacin da suke fafutukar gina kasa.

Yanzu haka Najeriya na fuskanyar matsalar tsaro da tashe-tashen hankali a kusan dukkan sassan kasar, kama daga hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas, da ayukan Fulani ‘yan bindiga a Arewa maso yamma, da rikicin kabilanci a Arewa ta tsakiya.

A yankin kudancin kasar ma akwai hare-hare kan hukumomi da jami’an tsaro da ake dangantawa da kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabas, kazalika da kai hare-hare kan ‘yan Arewa a yankin kudu maso yamma da dai sauransu.

Wannan yanayin ya janyo ra’ayoyi mabambanta tsakanin ‘yan kasar musamman masu fashin baki, wadanda suka soma bayyana ra’ayin cewa hakan kan iya kassara kasar.

Tuni kuma da aka sami rahotannin wasu ‘yan kasar a matakai daban-daban da suka soma kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da yayi murabus, ko kuma majalisar dokoki ta tsige shi, bisa zargin kasa shawo kan matsalar tsaron da ta addabi ‘yan Najeriya.

To sai dai a ra'ayin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, "ana iya kawo karshen wannan matsala muddin aka sami kishin kasa, kama daga shugabanni har ya zuwa daukacin ‘yan kasar baki daya."

Haka kuma ya bayyana samun fahimta da amincewa da juna, a bisa tsarin shugabanni su yi wa ‘yan kasa bayanin dukkan halin da ake ciki, yayin da su kuma ‘yan kasa su nuna fahimta da kuma aminci ga shugabanni.

Janar Babangida ya ce kamata yayi a yi amfani da darussan da aka koya a yakin basasa da Najeriyar ta kwashe tsawon watanni 18 tana gwabzawa a can baya, ta yadda za’a samo bakin zaren warware wannan matsalar tsaro da ake fama da ita a halin yanzu.

Ya kara da cewa duk da yake yanayin na yanzu ya bambanta da na lokacin yakin basasa, amma “muddin aka nuna kishin kasa da fahimta da kuma goyon bayan shugabanni, hakika za’a iya samun nasarar shawo kan wannan matsala.”

Da ya juya akan masu fafutukar ballewa domin kafa na su kasashen kuwa, Babangida ya ce kamata yayi a koyi darasi daga Abubuwan da suka faru a baya a Najeriya da ma yadda wasu kasashe suka tukari irin wannan matsala.

“Muna iya yin yadda kowa yayi ya sami nasara, idan da kishin kasa, za mu iya yin komai na tabbatar da kasarmu ta ci gaba da kasancewa daya, haka kuma ko wani ya ce zai balle ba zai sami nasara ba,” in ji Janar Ibrahim Babangida.

Saurari cikakkiyar tattaunawa da Janar Ibrahim Babangida:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsohon Shugaban Najeriya Ibrahim Babangida Akan Matsalar Tsaro