Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masallata 11 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Lokacin Sallar Tahajjud A Katsina Sun Kubuta


Wasu masallata suna sallah a Masallaci
Wasu masallata suna sallah a Masallaci

Akalla masallata 11 da suka hada da wani jariri da ‘yan bindiga suka yi awun gaba da su a yayin da suke tsaka da Ibadar Tahajjud sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga da suka sace su karamar hukumar Jibia.

Wata majiya daga jihar Katsina ne ta bayyana lamarin samun kubutar da mutanen daga hannun ‘yan bindiga a cewar rahotanni..

‘Yan bindigan sun sace masallatan 11 ne a ranar Litinin a wani masallaci da ke wajen garin Jibiya a yayin da suke tsaka da gudanar da ibadar watan Ramadan.

Majiyar wace ta yi magana da Channels, ta kuma kara da cewa, mutanen sun samu nasarar arcewa ne daga inda 'yan bindigan suka ajiye su a karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara a ranar Laraba.

A cewar wani da ya shaida lamarin, mutanen sun kubuta ne bayan da daya daga cikin matan da ke auren daya daga cikin 'yan bindigan ta taimaka wajen kunce musu igiyoyin da aka daure su tare da ba su umarnin su gudu.

Wadanda suka kubutan dai sun hada da maza 8 da mata 3 hade da jariri sai dai mace daya tilo da ta rage a can ita ce mahaifiyar jaririn da aka kubutar sakamakon yadda bata da karfin guduwa saboda kumburin kafaffun ta.

A halin yanzu dai, 'yan bindigan na neman kudin fansa na naira miliyan 10 kafin su sake ta.

Duk kokarin ji ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar dai ya ci tura a yayin hada wannan labari.

‘Yan bindiga dai sun dade suna addabar al’umman yankunan arewa maso yamma musamman jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da ma Neja lamarin da ake ganin kamar ya na neman gaggari gwamnatin Najeriya.

XS
SM
MD
LG