Za'a Gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya Bayani Game da Farmakin Da Aka Kai Kan Musulman Rohinga

myanmar hau do suan

Yayinda ake shirin gabatar da bayanin, shi kuma jakadan Myanmar a majalisar Dinkin Duniya bai yi na'am da wannan taron daza ayi ba yana ganin bashi da wani amfani.

Wani kwamiti na musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa¸ wanda ya zargi sojojin kasar Myanmar da aikata kisan kiyashi akan musulmai ‘yan Rohinga a shekarar da ta gabata, na shirin yiwa kwamitin sulhun majalisar bayani.

Kasashe tara ne daga cikin mambobi goma sha biyar na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, suka nemi a gana da shugaban kwamitin a hukuman ce, a cikin bukatar da suka mika shekaranjiya Talata.

Sai dai kuma jakadan Myanmar a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Hau Do Suan, ya nuna adawa da taron a wata wasika da ya aike ranar talata, inda yace ba wani abinda taron zai tsinana.

A wani rahoto da aka fitar a watan Agustan da ya wuce, kwamitin binciken ya ce ya gano hujjoji da suka nuna yanda sojojin Myanmar suka gudanar da kisan kare dangi akan musulman Rohingya.