Za'a fi Tuna Ariel Sharon da Kisan Gillar 1982 a Sabra da Shatila Inji Furofesa Boube Namaiwa

Wani tsohon hoton marigayi tsohon firai ministan Israila Ariel Sharon tare da matar shi Lily

Furofesa Boube Namaiwa ya ce da wuya kasashen duniya 'yan gurguzu masu akidar tausayawa talakawa su ji ko gezau
Bayan an bayar da labarin mutuwar tsohon firai ministan Israila Ariel Sharon Halima Djimrao ta tuntubi Furofesa Boube Namaiwa na jami'ar Cheikh Anta Diop ta birnin Dakar kasar Senegal, akan tarihin da marigayin ya bari da kum airin abubuwan da duniya za ta tuna shi da su:

Your browser doesn’t support HTML5

Furofesa Boube Namaiwa a kan mutuwar Ariel Sharon - 2:57


Ariel Sharon ya mutu ranar asabar ya na da shekaru tamanin da biyar, kuma bayan ya shafe shekaru takwas ya na kwance a asibiti cikin dogon suman da ya fitar da shi daga cikin hayyacin shi tun shekarar dubu biyu da shida sanadiyar toshewar jijiyar da ke kaiwa kwakwalwa jini.